Ibisobanuro bya qoran ntagatifu - Ibisobanuro bya Qur'an Ntagatifu mu rurimi rw'igihawusa - Abu Bakr Jomy.

external-link copy
57 : 17

أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا

Waɗancan, waɗanda suke kiran*, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce. info

* Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai.

التفاسير: