* Wanda ya yi wani abu da Allah Ya hana wajen ni'imõmi ko wajen wani abu dabam na sãɓon Allah, to, idan ya tũbã A gabãnin ya kai ga gargara, Allah zai gãfartã masa. Wannan ni'ima ce.
* Akwai daga ni'imõmin Allah,Ya sanya mutum maɗaukaki sabõda addininsa da ĩmãninsa ga Ubangijinsa, kuma Yã bã shi ĩkon binsa da taƙawa kamar yadda Ya yi wa Ibrahĩm. Kuma akwai daga ni'imõmin Allah Ya sanya mutum a cikin zuriyyar mutumin kirki kamar yadda Ya yi wa Annabi Muhammadu Ya sanya shi a cikin zuriyyar Ibrãhĩm.
* An ambaci Ibrãhĩm sabõda ya gõde wa ni'imõnin Allah dõmin Musulmi su yi kõyi da shi wajen gõde wa Allah ga ni'imõmin da Ya yi ishãra zuwa gare su a cikin wannan Sũra da watanta. Gõde wa ni'ima wata ni'ima ce.
* Yanã cikin ni'ima ga Ibrãhĩm da kammalarta a gare shi a umurci mafĩfĩcin tãlikai Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, da bin aƙĩdar Ibrãhĩm.
* Waɗanda suka sãɓa wa jũna a cikin sha'anin Ibrahĩm wanda yake ya kasance yanã girmama Juma'a dõmin ita ce rãnar cikon ni'imõmin Allah a kan bãyinsa. Yahudu suka sãɓã wa Ibrãhĩm suka girmama Asabar dõmin a rãnar nan ne bãbu wani aiki. Wannan ya dõge har a bãyan ɗauke Ĩsa. Nasãra suka jũya dõmin ƙin Yahũdu zuwa ga Lahadi, dõmin su yi daidai da Kaisara, Ƙustantin, mai girmama Lahadi, rãnar bautã wa rãnã. Kafirce wa ni'ima azaba ce.
* Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.
* Kuma mai kiran mutãne zuwa ga Allah lalle ne sai ya haɗu da cũtarwa daga mutãnen da bã su son gaskiyã. To, Allah bã Ya son zãlunci ko dã a kan maƙiyansa, sabõda haka Ya yi umurni da yin ƙisãsi da misãlin uƙũba, kõ a yi haƙuri, amma yin haƙuri yã fi rãmãwa dõmin nħman ni'imar Allah ta ƙãra kammala.