* Yahudu, ana kiran su da maganar Mũsa da ya ce wa Ubangiji, ‘Mun tuba zuwa gare Ka, yã Allah,’ (A’ãrãf, ãyã ta 155) dõmin izgili da suke yi na ƙin bin haddõdin Allah. Sunã karkatar da magana da asalin ma’anarta zuwa ga wata ma’ana ta izgili, sunã céwa ‘Mun ji’ amma aikinsu yanã nuna céwa, ‘Sun ƙi’ suke nufi. Kuma ‘Ka jiya a wanin wurin jiyãwa’ addu’a ce mai ɗaukar ma’anar alhẽri da ma’anar sharri, su kuwa sunã nufin ta sharrin. Haka kalmar ‘rã‘ina’ tanã da ma’anar ‘tsãre mu’ ko ‘saurãra mana’, kuma tanã da ma’anar ‘Yã ruɓaɓɓe'. Sunã nufin ma’anar ƙarshen. Wannan bayãni’ shi ma taimako ne ga Musulmi mãsu raunin hankali dõmin a tsare musu addininsu kamar yadda ake tsaron dũkiyarsu. An cũsa irin wannan mãkirci a wata addu’a da suke cewa ‘Jauharatul Kamãli’ inda suka sifanta wanda suke yi wa salãti da “asƙam” mafi cũta. Wannan tã yi daidai da kalmar rã’ina, ko ma ta fi mũni, dõmin rã’ina tanã da wata ma’ana ta yabo, amma asƙam bã ta da wata ma'ana sai ta zãgi kawai. Allah Ya tsare mu daga sharrin maƙiyan addini.
* Jibti sunan kowane gunki ne.Ɗãgũtu sunan Shaiɗan ne mai ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, sheɗãnin da yake zama tare da gumãka ko waninsu, mutum ne ko aljani, dõmin ya ɓatar da mãsu raunin hankali, a cikin Yahũdu ko a cikin Musulmi.