Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi

Saba'i

external-link copy
1 : 34

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 34

يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۚ وَهُوَ ٱلرَّحِيمُ ٱلۡغَفُورُ

Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 34

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَأۡتِينَا ٱلسَّاعَةُۖ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتَأۡتِيَنَّكُمۡ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِۖ لَا يَعۡزُبُ عَنۡهُ مِثۡقَالُ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَآ أَصۡغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡبَرُ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 34

لِّيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِۚ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 34

وَٱلَّذِينَ سَعَوۡ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مِّن رِّجۡزٍ أَلِيمٞ

Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyin Mu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 34

وَيَرَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ ٱلۡحَقَّ وَيَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ

Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 34

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هَلۡ نَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ يُنَبِّئُكُمۡ إِذَا مُزِّقۡتُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمۡ لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدٍ

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?" info
التفاسير: