Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi

Número de página:close

external-link copy
56 : 22

ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 22

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyin Mu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa. info
التفاسير:

external-link copy
58 : 22

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ

Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa. info
التفاسير:

external-link copy
59 : 22

لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri. info
التفاسير:

external-link copy
60 : 22

۞ ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. info
التفاسير:

external-link copy
61 : 22

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani. info
التفاسير:

external-link copy
62 : 22

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
63 : 22

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَتُصۡبِحُ ٱلۡأَرۡضُ مُخۡضَرَّةًۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ

Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa* daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa. info

* Ya misalta Alƙur'ãni da ruwan girgije. Kamar yadda ruwa ke sauka daga sama ya rãya ƙasã haka Alƙur'ãni yake sauka ya rãya zukãta.

التفاسير:

external-link copy
64 : 22

لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shi ne wadatacce, Gõdadde. info
التفاسير: