Tradução dos significados do Nobre Qur’an. - tradução Hawsia - Abu Bakr Jumi

external-link copy
127 : 20

وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَنۡ أَسۡرَفَ وَلَمۡ يُؤۡمِنۢ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦۚ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبۡقَىٰٓ

Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa info

* Wanda ya yawaita, shi ne Musulmi fãsiƙi kõ mai bidi'a yanã ƙara abin da ba a sani ba a cikin addini, ya yawaita shi. Shi ma ya shiga a cikin wahalar dũniya. Kuma ta Lãhira ta fi tsanani.

التفاسير: