Kilniojo Korano reikšmių vertimas - Vertimas į hausų k. - Abu Bakr Džūmi

Al'munafikoun

external-link copy
1 : 63

إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ قَالُواْ نَشۡهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَكَٰذِبُونَ

Idan munãfukai* suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa Manzon Sa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne. info

* Munãfuki, a zãmanin Annabi, shine wanda ya bayyana Musulunci, amma kuma a ɓõye Shĩ kãfiri ne. A bãyan Annabi anã cewa munãfuki zindĩƙi.

التفاسير: