* Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.
* A lõkacin da Ƙuraishi suka ga bã su iya yãƙi da Annabi, suka dõge da ƙabĩlancinsu, ta hanyar sulhu. Suka aika sahlu bn Amru da Huwaitib bn Abdul Uzza da Makraz bn Hafs bn Ahnaf dõmin neman sulhu bisa kada Annabi ya shiga Makka a wannan shekara, amma shekara mai kõmõwa ya je ya shiga Makka kwana uku, su kuma su fita har ya ƙãre Umra ya fita. Annabi ya karɓi sulhun. Aka ce Aliyu bn Abi Talib ya rubũta. Wajen rubũtun kuma aka so a yi tãshin hankali, dõmin ya rũbuta, Manzon Allah ya yi sulhu da Ƙuraishãwa, sai kuma suka ce ba su yarda a rubũta kalmar Manzon Allah ba. Sai Annabi ya sanya hannunsa mai daraja ya sõke kalmar da ake sãɓãni a kanta. Allah Ya saukar da natsuwa ga kõwa. ** Kalmar taƙawa ita ce kalmar shahãda dõmin ɗaukar alkawari da ita yanã lazimtawa mai ita bin umurnin Allah da dãɗi kõ ba daɗi ta haka sai natsuwa ta sãmu. Anã ce mata kalmar taƙawa dõmin da ita ake kãre rai daga bin shaiɗan. Ma'anar taƙawa, ita ce kãriya.