* Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Ulũhiyya ne da Rubũbiyya. Fitar mutãne daga asali guda, wanda bãbu wani surki a cikinsa yana wajabtar da girman jinsin mutum, kõwane iri ne, kowane launi, kuma kõwace halitta yake ɗauke da ita.Tsõron Allah da tsaronSa a kan mutãne yana wajabtar da tsayãwa a cikin haddõdin sharĩ'arSa. Tsõron zumunta ko rantsuwa da ita yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah na kusa da na nesa. Hadĩsi ya nũna ba a yin rantsuwa da wanin Allah sabõda haka ma'anar aya itace, 'Ku ji tsõron Allah ku tsare mahaifa da zumunta!'.
* Asalin marãya shĩ ne yãron da bai balaga ba, kuma ubansa ya mutu. Amma a cikin ãya-Allah Yã sani-anã nufin dukkan mai rauni a cikin al'umma, wanda yake neman a tsare haƙƙin sa da Allah Ya ɗõra wa Musulmi su tsare. Sabõda haka Ya shãfe jawãbin sharaɗin kuma Ya fãra da hukunce-hukunce, a kan tafsĩlin yadda zã a tsare mãsu rauni a cikin al'umma. Ya fãra da mãta a wajen aure, adadinsu daga ɗaya zuwa huɗu, gwargwadon ƙarfin mutum da iyãwarsa ga tsaida ãdalci a gare su, kõ a tsakãninsu. Ãdalci na kwãna da ciyarwa da tufãtarwa.
* Sa'an nan yadda ake riƙon dũkiyar wãwã wanda bai san yadda ake riƙon dũkiya ba, ko dã shĩ bãligi ne, yã yi aure, kuma ko da shĩ ne yake neman dũkiyarsa da kansa; kamar da ijãra. Wannan wata hanyace ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.