* Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla. ** Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye.
* Alfãshar mutãnen Lũɗu, ita ce luwãɗi, namji yabi namiji a duburarsa wannan alfãsha, kõ dabbõbi bã su yin ta. Ga mutãnen Lũɗuta fãra bayyana. Allah Ya halakar da su kamar yadda Ya ambata. Sa'an nan kuma ba a ƙãra ganinta ba, sai ga wannan al'umma asĩirin da ke ciki, shĩ ne yadda Allah Yake jũyar da ɗabĩ'ar mutum ta zama bã ta mãsu hankali ba, tãre da dõgewar halittar jikinsa kamar yadda take ga zãhiri.