* Misãlin sãɓãni tsakãninsu; Nasãra suka taimaki Bukhta Nassara ga ɓata masallacin Baitil Maƙdis da jefa mũshe da shãra a ciki, dõmin ƙin Yahũdu. Wannan ƙiyayya tã bayyana har a cikin takardar alƙawari a tsakãnin Nasãra da Halifa Umar bn Khattãb suka ce kada ya bar Yahũdu su shiga Baitil Maƙdis. Sabõda haka idan wasu sun hana ku isa ga masallacinku kõ kuma suka jũyarda ku daga Alƙibla, to, kada ku ji kõme, sun yi irin aikin danginsu. Gabas da yamma na Allah ɗaya ne, duk inda aka jũyar da ku, to, a can yardar Allah take. A lõkacin Musulmi na dũbin Baitil Maƙdis ga salla a bãyan Hijira daga Makka, bã su son haka.