وه‌رگێڕانی ماناكانی قورئانی پیرۆز - وەرگێڕاوی هەوساوی - ئەبوبەکر جومی

ژمارەی پەڕە:close

external-link copy
67 : 17

وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِي ٱلۡبَحۡرِ ضَلَّ مَن تَدۡعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ أَعۡرَضۡتُمۡۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ كَفُورًا

Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci. info
التفاسير:

external-link copy
68 : 17

أَفَأَمِنتُمۡ أَن يَخۡسِفَ بِكُمۡ جَانِبَ ٱلۡبَرِّ أَوۡ يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗا ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ وَكِيلًا

Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku? info
التفاسير:

external-link copy
69 : 17

أَمۡ أَمِنتُمۡ أَن يُعِيدَكُمۡ فِيهِ تَارَةً أُخۡرَىٰ فَيُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ قَاصِفٗا مِّنَ ٱلرِّيحِ فَيُغۡرِقَكُم بِمَا كَفَرۡتُمۡ ثُمَّ لَا تَجِدُواْ لَكُمۡ عَلَيۡنَا بِهِۦ تَبِيعٗا

Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi. info
التفاسير:

external-link copy
70 : 17

۞ وَلَقَدۡ كَرَّمۡنَا بَنِيٓ ءَادَمَ وَحَمَلۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ كَثِيرٖ مِّمَّنۡ خَلَقۡنَا تَفۡضِيلٗا

Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam*, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa. info

* Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da sauran halittar Allah.

التفاسير:

external-link copy
71 : 17

يَوۡمَ نَدۡعُواْ كُلَّ أُنَاسِۭ بِإِمَٰمِهِمۡۖ فَمَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ يَقۡرَءُونَ كِتَٰبَهُمۡ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلٗا

A rãnar da Muke kiran* kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno. info

* Muƙãrana a Lãhira a tsakãnin al'ummõmi kuma da tsakãnin mũminai da kãfirai,.

التفاسير:

external-link copy
72 : 17

وَمَن كَانَ فِي هَٰذِهِۦٓ أَعۡمَىٰ فَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ أَعۡمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلٗا

Kuma wanda ya kasance makãho* a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya. info

* Muƙarana a tsakãnin makantar basĩra da makantar ganin ido.

التفاسير:

external-link copy
73 : 17

وَإِن كَادُواْ لَيَفۡتِنُونَكَ عَنِ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ لِتَفۡتَرِيَ عَلَيۡنَا غَيۡرَهُۥۖ وَإِذٗا لَّٱتَّخَذُوكَ خَلِيلٗا

Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi. info
التفاسير:

external-link copy
74 : 17

وَلَوۡلَآ أَن ثَبَّتۡنَٰكَ لَقَدۡ كِدتَّ تَرۡكَنُ إِلَيۡهِمۡ شَيۡـٔٗا قَلِيلًا

Kuma bã dõmin* Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan. info

* Muƙãrana a tsakãnin sarauta da Manzancin Allah. Sarkin dũniya yanã canja manufarsa dõmin neman yardar mutãnensa. Amman Manzon Allah bã ya sãke abin da Allah Ya umurce shi da shi dõmin neman yardar Mutãne.

التفاسير:

external-link copy
75 : 17

إِذٗا لَّأَذَقۡنَٰكَ ضِعۡفَ ٱلۡحَيَوٰةِ وَضِعۡفَ ٱلۡمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيۡنَا نَصِيرٗا

A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu. info
التفاسير: