* Kamar yadda littattafan farko suke, haka Alƙur'ãni yake daga Allah, sai dai shi Alƙur'ãni an saukar da shi a cikin Lãrabci.
* Aikõwar Manzanni da littattafai ba ya hana Allah Ya aiko wani Manzo daga bãya da wani littãfi wanda ya shãfe abin da yake cikin littattafan farko. Allah Yã tabbatar da abin da yake so na hukunce-hukuncen da suka gabãta dõmin dõgewar aikinsu ga mutãne har yanzu, kuma Ya shãfe abin da yake so sabõda amfãninsu da hukuncinsu yã shige, sabõda wata hikima da Allah Ya sani amma asalin littattãfan duka wanda bã zai canja ba a cikin sanin Allah, yanã wurinsa.".
* Idan Mun so Mu yi musu azãba a gaban idonka zã Mu yi musu, kuma idan Mun so Mu jinkirta musu har a bãyan ka mutu, wannan bã aikinka ba ne, Nãmu ne. Abin da yake aikinka shĩ ne iyar da manzanci kawai. Yin hisãbi a kansu alhakin Allah ɗai ne.
* Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhħri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhħri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa.