クルアーンの対訳 - ハウサ語対訳 - Abu Bakr Jomy

Abasa

external-link copy
1 : 80

عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ

Yã game huska* kuma ya jũya bãya. info

* Wani makãho, Abdullahi bin Ummi Maktũm ya je wurin Annabi dõmin ya musulunta, sai ya iske a lõkacin nan Annabi na ƙõƙarin shiryar da wasu manyan mutãne na Ƙuraishãwa, sai wannan makãhon ya yanke maganar Annabi da su, bã da saninsa ba, alhãli Annabi na bũrin su musulunta dõmin darajarsu ga idon mutãnensu. Saboda haka Annabi, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ɓata Fuska, ya tafi dõmin ɓacin ransa, saboda rashin musuluntarsu. Bãyan haka Annabi nã girmama Abdullahi ƙwarai, idan ya je wurinsa sai ya ce masa "Maraba da wanda Ubangijina Ya zarge ni sabõda shi." Kuma ya shimfiɗa masa mayafinsa, idan ya fita tafiya, yakan sanya shi riƙon garin Madina, ƙissar tana nũna girmamawar Allah ga Annabi da Ya ce: "Ya game Fuska." Bai ce masa: "Domin ka game Fuska" ba, sai ya faɗa a cikin hali mai sauƙi.".

التفاسير:

external-link copy
2 : 80

أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ

Sabõda makãho yã je masa. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 80

وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ

To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 80

أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ

Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? info
التفاسير:

external-link copy
5 : 80

أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ

Amma wanda ya wadãtu da dũkiya. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 80

فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ

Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi! info
التفاسير:

external-link copy
7 : 80

وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ

To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba? info
التفاسير:

external-link copy
8 : 80

وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ

Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 80

وَهُوَ يَخۡشَىٰ

Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 80

فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ

Kai kuma kã shagala ga barinsa! info
التفاسير:

external-link copy
11 : 80

كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ

A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 80

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah). info
التفاسير:

external-link copy
13 : 80

فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ

(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa, info
التفاسير:

external-link copy
14 : 80

مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ

Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 80

بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ

A cikin hannãyen mala'iku marubũta. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 80

كِرَامِۭ بَرَرَةٖ

Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 80

قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ

An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! info
التفاسير:

external-link copy
18 : 80

مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ

Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 80

مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ

Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). info
التفاسير:

external-link copy
20 : 80

ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ

Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 80

ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ

Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 80

ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ

Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 80

كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ

Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). info
التفاسير:

external-link copy
24 : 80

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ

To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 80

أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا

Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 80

ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا

Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 80

فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا

Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 80

وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا

Da inabi da ciyãwa. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 80

وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا

Da zaitũni da itãcen dabĩno. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 80

وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا

Da lambuna, mãsu yawan itãce. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 80

وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا

Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 80

مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ

Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 80

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ

To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 80

يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ

Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 80

وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ

Da uwarsa da ubansa. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 80

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ

Da mãtarsa da ɗiyansa. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 80

لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ

Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 80

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ

Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 80

ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ

Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 80

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ

Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu. info
التفاسير:

external-link copy
41 : 80

تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ

Baƙi zai rufe su. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 80

أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ

Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu). info
التفاسير: