クルアーンの対訳 - ハウサ語対訳 - Abu Bakr Jomy

ページ番号:close

external-link copy
40 : 26

لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ

"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya." info
التفاسير:

external-link copy
41 : 26

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُواْ لِفِرۡعَوۡنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ

To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?" info
التفاسير:

external-link copy
42 : 26

قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai." info
التفاسير:

external-link copy
43 : 26

قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ

Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa." info
التفاسير:

external-link copy
44 : 26

فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." info
التفاسير:

external-link copy
45 : 26

فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ

Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya. info
التفاسير:

external-link copy
46 : 26

فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ

Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada. info
التفاسير:

external-link copy
47 : 26

قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta." info
التفاسير:

external-link copy
48 : 26

رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

"Ubangijin Mũsa da Hãrũna." info
التفاسير:

external-link copy
49 : 26

قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ

Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya." info
التفاسير:

external-link copy
50 : 26

قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ

Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu." info
التفاسير:

external-link copy
51 : 26

إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni." info
التفاسير:

external-link copy
52 : 26

۞ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ

Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne. info

* Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu.

التفاسير:

external-link copy
53 : 26

فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ

Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 26

إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٞ قَلِيلُونَ

"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan." info
التفاسير:

external-link copy
55 : 26

وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ

"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne." info
التفاسير:

external-link copy
56 : 26

وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ

"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne." info
التفاسير:

external-link copy
57 : 26

فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ

Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari. info
التفاسير:

external-link copy
58 : 26

وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ

Da taskõki da mazauni mai kyau. info
التفاسير:

external-link copy
59 : 26

كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ

Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla. info
التفاسير:

external-link copy
60 : 26

فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ

Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã. info
التفاسير: