Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Al'lail

external-link copy
1 : 92

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ

Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 92

وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ

Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 92

وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ

Da abin da ya halitta namiji da mace. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 92

إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ

Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 92

فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ

To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 92

وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ

Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo. info

* Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan Manzon Sa, shi ne taƙawa.

التفاسير:

external-link copy
7 : 92

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ

To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 92

وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ

Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 92

وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ

Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 92

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ

To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 92

وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ

Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). info
التفاسير:

external-link copy
12 : 92

إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ

Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 92

وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ

Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 92

فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارٗا تَلَظَّىٰ

Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 92

لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى

Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa info
التفاسير:

external-link copy
16 : 92

ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 92

وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى

Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta. info

* Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi.

التفاسير:

external-link copy
18 : 92

ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ

Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 92

وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٖ تُجۡزَىٰٓ

Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 92

إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 92

وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ

To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi). info
التفاسير: