Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Al'nazi'at

external-link copy
1 : 79

وَٱلنَّٰزِعَٰتِ غَرۡقٗا

Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 79

وَٱلنَّٰشِطَٰتِ نَشۡطٗا

Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 79

وَٱلسَّٰبِحَٰتِ سَبۡحٗا

Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 79

فَٱلسَّٰبِقَٰتِ سَبۡقٗا

Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 79

فَٱلۡمُدَبِّرَٰتِ أَمۡرٗا

Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 79

يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ

Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 79

تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ

Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 79

قُلُوبٞ يَوۡمَئِذٖ وَاجِفَةٌ

Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 79

أَبۡصَٰرُهَا خَٰشِعَةٞ

Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 79

يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِي ٱلۡحَافِرَةِ

Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? info
التفاسير:

external-link copy
11 : 79

أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا نَّخِرَةٗ

"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" info
التفاسير:

external-link copy
12 : 79

قَالُواْ تِلۡكَ إِذٗا كَرَّةٌ خَاسِرَةٞ

Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" info
التفاسير:

external-link copy
13 : 79

فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ

To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 79

فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ

Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 79

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ

Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? info
التفاسير:

external-link copy
16 : 79

إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى

A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? info
التفاسير: