Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Al'dukhan

external-link copy
1 : 44

حمٓ

Ḥ. M̃. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 44

وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 44

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةٖ مُّبَٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ

Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 44

فِيهَا يُفۡرَقُ كُلُّ أَمۡرٍ حَكِيمٍ

A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 44

أَمۡرٗا مِّنۡ عِندِنَآۚ إِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ

Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 44

رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 44

رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). info
التفاسير:

external-link copy
8 : 44

لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 44

بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ يَلۡعَبُونَ

A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 44

فَٱرۡتَقِبۡ يَوۡمَ تَأۡتِي ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٖ مُّبِينٖ

Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 44

يَغۡشَى ٱلنَّاسَۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٞ

Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 44

رَّبَّنَا ٱكۡشِفۡ عَنَّا ٱلۡعَذَابَ إِنَّا مُؤۡمِنُونَ

Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 44

أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكۡرَىٰ وَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مُّبِينٞ

Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? info
التفاسير:

external-link copy
14 : 44

ثُمَّ تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَقَالُواْ مُعَلَّمٞ مَّجۡنُونٌ

Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci." info

* Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali.

التفاسير:

external-link copy
15 : 44

إِنَّا كَاشِفُواْ ٱلۡعَذَابِ قَلِيلًاۚ إِنَّكُمۡ عَآئِدُونَ

Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). info
التفاسير:

external-link copy
16 : 44

يَوۡمَ نَبۡطِشُ ٱلۡبَطۡشَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ

Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 44

۞ وَلَقَدۡ فَتَنَّا قَبۡلَهُمۡ قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَ وَجَآءَهُمۡ رَسُولٞ كَرِيمٌ

Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 44

أَنۡ أَدُّوٓاْ إِلَيَّ عِبَادَ ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." info
التفاسير: