* Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u.
* Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu.