Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Al'naba'i

external-link copy
1 : 78

عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ

A kan mẽ suke tambayar jũna? info
التفاسير:

external-link copy
2 : 78

عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ

A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)? info
التفاسير:

external-link copy
3 : 78

ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ

Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa? info
التفاسير:

external-link copy
4 : 78

كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ

A'aha! Zã su sani. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 78

ثُمَّ كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ

Kuma, a'aha! Zã su sani. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 78

أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا

Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba? info
التفاسير:

external-link copy
7 : 78

وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا

Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)? info
التفاسير:

external-link copy
8 : 78

وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجٗا

Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã? info
التفاسير:

external-link copy
9 : 78

وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتٗا

Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa? info
التفاسير:

external-link copy
10 : 78

وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا

Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura? info
التفاسير:

external-link copy
11 : 78

وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشٗا

Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci? info
التفاسير:

external-link copy
12 : 78

وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعٗا شِدَادٗا

Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi? info
التفاسير:

external-link copy
13 : 78

وَجَعَلۡنَا سِرَاجٗا وَهَّاجٗا

Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)? info
التفاسير:

external-link copy
14 : 78

وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءٗ ثَجَّاجٗا

Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba? info
التفاسير:

external-link copy
15 : 78

لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبّٗا وَنَبَاتٗا

Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? info
التفاسير:

external-link copy
16 : 78

وَجَنَّٰتٍ أَلۡفَافًا

Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? info
التفاسير:

external-link copy
17 : 78

إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتٗا

Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 78

يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجٗا

Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 78

وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبٗا

Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 78

وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا

Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 78

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادٗا

Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 78

لِّلطَّٰغِينَ مَـَٔابٗا

Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 78

لَّٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابٗا

Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 78

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدٗا وَلَا شَرَابًا

Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 78

إِلَّا حَمِيمٗا وَغَسَّاقٗا

Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 78

جَزَآءٗ وِفَاقًا

Sakamako mai dãcẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 78

إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابٗا

Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 78

وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابٗا

Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa! info
التفاسير:

external-link copy
29 : 78

وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا

Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 78

فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا

Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 78

إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا

Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 78

حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبٗا

Lambuna da inabõbi. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 78

وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابٗا

Da yan Mata tsaraikun Juna info
التفاسير:

external-link copy
34 : 78

وَكَأۡسٗا دِهَاقٗا

Da hinjãlan giya cikakku. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 78

لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا كِذَّٰبٗا

Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 78

جَزَآءٗ مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابٗا

Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 78

رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابٗا

Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 78

يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ صَفّٗاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابٗا

Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 78

ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا

Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 78

إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابٗا قَرِيبٗا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا

Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!" info
التفاسير: