* Ku bi umurnin Allah kamar yadda Ya aza muku hukunce-hukuncenSa, kada ku karkace da bin umurnin waɗansu na dabam waɗanda bã Allah ba, kõ kuma kada ku bi son zũciyarku. Bin umurnin wani zai sanya ku sãɓãwa jũnanku, ku rarrabu, ku rasa ƙarfi a kan maƙiyanku. Wanda ya bi umurnin waɗansu, waɗanda bã Allah ba, to ya yi shirka da Allah ke nan kuma haɗuwar mãsu bin umurnin waɗansu waɗanda bã Allah ba, to, tanã da wuya. Wannan ãya ta hana bin ɗarĩƙõƙin ƙungiyõyin sũfãye duka, dõmin bin su, bin umurnin waɗansu ne waɗanda bã Allah ba kuma yanã rarraba Musulmi, su zama ƙungiya-ƙungiya, da sãɓãni mai nĩsa. Bã zã a ce ba, "Ã'aha! Wannan ãya ta sauka ga Yahũdu da Nasãra kawai" dõmin ãyõyi biyu l4 da l5, mãsu bin wannan, sun gama harda Musulmi, dõmin umurni ga Annabi, umarni ne sabõda al'ummarsa. Kuma sãɓãnin mãsu ɗariƙõƙi sãɓãni ne a kan asali watau aƙida, bã sãɓãnine a kan rassuna na furũ'a ba. Sabõda haka bãbu ƙiyayya a tsakãnin mabiya mazhabõbi, dõmin sãɓãninsu, na fahimta ne kawai. Sãɓãni ga reshe, rahama ce, amma sãɓãni ga asali azãba ce. ** Watau haɗuwar jama'a ga bin addini guda, bã da sãɓawa ba ga asalinsa. Wanda ya ce: An saukar wa wani mutum, baicin Muhammadu, da wani abu daga Allah, to, shĩ ya sãɓãwa asali. Sãɓãwa ga asali kãfirci ne.
* Kalmar da ta gabãta, ita ce "Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo." Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala.