Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Numéro de la page:close

external-link copy
6 : 30

وَعۡدَ ٱللَّهِۖ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 30

يَعۡلَمُونَ ظَٰهِرٗا مِّنَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ عَنِ ٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ غَٰفِلُونَ

Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.* info

* Dangantakar rashin sanin ĩkon Allah da sanin sha'anin dũniya da kuma jãhiltar al'amarin Lãhira,.

التفاسير:

external-link copy
8 : 30

أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَآيِٕ رَبِّهِمۡ لَكَٰفِرُونَ

Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya* da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu? info

* Gaskiya ita ce tsãri tabbatacce wanda bã ya canzãwa.

التفاسير:

external-link copy
9 : 30

أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَأَثَارُواْ ٱلۡأَرۡضَ وَعَمَرُوهَآ أَكۡثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 30

ثُمَّ كَانَ عَٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَٰٓـُٔواْ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ بِهَا يَسۡتَهۡزِءُونَ

Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 30

ٱللَّهُ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 30

وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبۡلِسُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 30

وَلَمۡ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمۡ شُفَعَٰٓؤُاْ وَكَانُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwa daga abũbuwan shirkinsu. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 30

وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَتَفَرَّقُونَ

kuma a rãnar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 30

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَهُمۡ فِي رَوۡضَةٖ يُحۡبَرُونَ

To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu. info
التفاسير: