Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Al'qasas

external-link copy
1 : 28

طسٓمٓ

T. S̃. M̃. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 28

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 28

نَتۡلُواْ عَلَيۡكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرۡعَوۡنَ بِٱلۡحَقِّ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 28

إِنَّ فِرۡعَوۡنَ عَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلَ أَهۡلَهَا شِيَعٗا يَسۡتَضۡعِفُ طَآئِفَةٗ مِّنۡهُمۡ يُذَبِّحُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَيَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 28

وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنَجۡعَلَهُمۡ أَئِمَّةٗ وَنَجۡعَلَهُمُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda. info
التفاسير: