Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Numéro de la page:close

external-link copy
25 : 21

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ

Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini." info
التفاسير:

external-link copy
26 : 21

وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ

Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 21

لَا يَسۡبِقُونَهُۥ بِٱلۡقَوۡلِ وَهُم بِأَمۡرِهِۦ يَعۡمَلُونَ

Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurnin Sa suke aiki. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 21

يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ

Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõron Sa. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 21

۞ وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّٰلِمِينَ

Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 21

أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ

Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,* sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba? info

* Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, Kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi.

التفاسير:

external-link copy
31 : 21

وَجَعَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِهِمۡ وَجَعَلۡنَا فِيهَا فِجَاجٗا سُبُلٗا لَّعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ

Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 21

وَجَعَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ سَقۡفٗا مَّحۡفُوظٗاۖ وَهُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهَا مُعۡرِضُونَ

Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 21

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ

Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu* a cikin wani sarari suKe iyo. info

* Wannan yã nũna cewa rãnã da watã a cikin sarari guda suke, Kõ da yake akwai nĩsan gaske a tsakãninsu.

التفاسير:

external-link copy
34 : 21

وَمَا جَعَلۡنَا لِبَشَرٖ مِّن قَبۡلِكَ ٱلۡخُلۡدَۖ أَفَإِيْن مِّتَّ فَهُمُ ٱلۡخَٰلِدُونَ

Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama? info
التفاسير:

external-link copy
35 : 21

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku. info
التفاسير: