Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

external-link copy
204 : 2

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعۡجِبُكَ قَوۡلُهُۥ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيُشۡهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِي قَلۡبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلۡخِصَامِ

Kuma akwai daga mutãne* wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne. info

* Bayãnin munafuki da hãlayensa, a cikin jama'a, a san shi, dõmin kada a dõgara a kansa. Haka mutumin kirki shi ma ana son a san shi dõmin a dogara da shi kamar yadda yayi bayãninsa.

التفاسير: