* Wannan ƙissa tana nũna cewa ba a iya yin yãƙi sai da sarki' shũgaba. Kuma ta fadi dalĩlin da ke sanya jama'a su yi yãƙi; watau dõmin tsaron addini da rãyuka da nasaba da mutunci da dũkiya.
* Sũnan Annabinsu Shamwĩlu daga Sibt Lãwaya. A bãyan Mũsã Yũsha'u bin Nũn sa'an nan Kãlib, sa'an nan Hizƙĩl, sa'an nan Ilyas sa'an nan Alyasa'u, daga nan Bani Isrã'ila suka rasa mai jan su har Amãliƙa ɗiyan Amlĩƙ bn Ãd waɗanda ke zaune a Falastĩn suka rinjãyi Bani Isrã'ila, suka karkashe su suka kõre su daga gidãjensu suka kãma 'ya'yansu, har a lõkacin da wata mace daga Sibt Lãwaya ta haifi Shamwĩlu Annabi. Ya naɗa musu sarki Ɗãlũta.** Ɗãlũta yana a cikin gidan Binyãminu ɗan Ya'aƙũbu talakãwa ne sunã dõgara a kan sanã'a. Zũriyyar Yahũza, sũ ne sarãkuna dõmin haka sunansu ya rinjãya a kan Bani Isra'ila. Zũriyyar Lãwaya sũ ne Annabãwa da mãlamai.
* Akwatin Natsuwa, an saukar da shi tãre da Ãdam a cikinsa akwai sũrõrin annabãwa, da gãdon riƙonsa ya kai ga Mũsã yanã sanya Attaura a ciki sabõda haka aka sãmi karyayyun allunan Attaura a ciki da rawanin Harũna da wani abu daga Mannu da Salwa. A lõkacin da Amãliƙa suka rinjãye su, sai suka karɓe wannan akwãti suka ajiye shi inda bai dãce da shi ba, har a lõkacin da malã'iku suka ɗauke shi zuwa ga Ɗãlũta.