Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Al'fatiha

external-link copy
1 : 1

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; info
التفاسير:

external-link copy
3 : 1

ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Mai rahama, Mai jin ƙai; info
التفاسير:

external-link copy
4 : 1

مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 1

إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ

Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa info
التفاسير:

external-link copy
6 : 1

ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 1

صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ

Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.* info

* Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgewa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.

التفاسير: