Firo maanaaji al-quraan tedduɗo oo - Eggo (nantino) ngoo e Hawsaare - Abubakar Gummi

Tonngoode hello ngoo:close

external-link copy
160 : 26

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
161 : 26

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" info

* Lũɗu ɗan'uwansu ne na zaman gari da aure kawai. Asalinsa ɗan baffan Ibrãhĩm ne, sun tãso daga gabas, ƙasar Bãbila suka yi hijira, har ibrahĩm ya sauka Habrũna a ƙasar Shãm, Lũɗu kuwa ya sauka a sadũm da alƙaryunta.

التفاسير:

external-link copy
162 : 26

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce." info
التفاسير:

external-link copy
163 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
164 : 26

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
165 : 26

أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?" info
التفاسير:

external-link copy
166 : 26

وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ

"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!" info
التفاسير:

external-link copy
167 : 26

قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ

Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)." info
التفاسير:

external-link copy
168 : 26

قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ

Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa." info
التفاسير:

external-link copy
169 : 26

رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ

"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
170 : 26

فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ

Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya. info
التفاسير:

external-link copy
171 : 26

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ

Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa. info
التفاسير:

external-link copy
172 : 26

ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ

Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu. info
التفاسير:

external-link copy
173 : 26

وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ

Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. info
التفاسير:

external-link copy
174 : 26

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
175 : 26

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
176 : 26

كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
177 : 26

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ شُعَيۡبٌ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" info
التفاسير:

external-link copy
178 : 26

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce." info
التفاسير:

external-link copy
179 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
180 : 26

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
181 : 26

۞ أَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُخۡسِرِينَ

"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)." info
التفاسير:

external-link copy
182 : 26

وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ

"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce." info
التفاسير:

external-link copy
183 : 26

وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ

"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna." info
التفاسير: