Firo maanaaji al-quraan tedduɗo oo - Eggo (nantino) ngoo e Hawsaare - Abubakar Gummi

Tonngoode hello ngoo:close

external-link copy
20 : 26

قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذٗا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ

Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi." info
التفاسير:

external-link copy
21 : 26

فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمٗا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni." info
التفاسير:

external-link copy
22 : 26

وَتِلۡكَ نِعۡمَةٞ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ

"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla." info
التفاسير:

external-link copy
23 : 26

قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?" info
التفاسير:

external-link copy
24 : 26

قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 26

قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ

Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?" info
التفاسير:

external-link copy
26 : 26

قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko." info
التفاسير:

external-link copy
27 : 26

قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِيٓ أُرۡسِلَ إِلَيۡكُمۡ لَمَجۡنُونٞ

Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne." info
التفاسير:

external-link copy
28 : 26

قَالَ رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ

Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta." info
التفاسير:

external-link copy
29 : 26

قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذۡتَ إِلَٰهًا غَيۡرِي لَأَجۡعَلَنَّكَ مِنَ ٱلۡمَسۡجُونِينَ

Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru." info
التفاسير:

external-link copy
30 : 26

قَالَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكَ بِشَيۡءٖ مُّبِينٖ

Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?" info
التفاسير:

external-link copy
31 : 26

قَالَ فَأۡتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya." info
التفاسير:

external-link copy
32 : 26

فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ

Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 26

وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ

Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 26

قَالَ لِلۡمَلَإِ حَوۡلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ

(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi! info
التفاسير:

external-link copy
35 : 26

يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِۦ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ

"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?" info
التفاسير:

external-link copy
36 : 26

قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَٱبۡعَثۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ

Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne." info
التفاسير:

external-link copy
37 : 26

يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٖ

"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani." info
التفاسير:

external-link copy
38 : 26

فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ

Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 26

وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلۡ أَنتُم مُّجۡتَمِعُونَ

Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne? info
التفاسير: