ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمهه‌ى هوساوى - ابوبكر جومى

شماره صفحه:close

external-link copy
34 : 8

وَمَا لَهُمۡ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ ٱللَّهُ وَهُمۡ يَصُدُّونَ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَمَا كَانُوٓاْ أَوۡلِيَآءَهُۥٓۚ إِنۡ أَوۡلِيَآؤُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُتَّقُونَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 8

وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمۡ عِندَ ٱلۡبَيۡتِ إِلَّا مُكَآءٗ وَتَصۡدِيَةٗۚ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ

Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 8

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ لِيَصُدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيۡهِمۡ حَسۡرَةٗ ثُمَّ يُغۡلَبُونَۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحۡشَرُونَ

Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su; info
التفاسير:

external-link copy
37 : 8

لِيَمِيزَ ٱللَّهُ ٱلۡخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ وَيَجۡعَلَ ٱلۡخَبِيثَ بَعۡضَهُۥ عَلَىٰ بَعۡضٖ فَيَرۡكُمَهُۥ جَمِيعٗا فَيَجۡعَلَهُۥ فِي جَهَنَّمَۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 8

قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِن يَنتَهُواْ يُغۡفَرۡ لَهُم مَّا قَدۡ سَلَفَ وَإِن يَعُودُواْ فَقَدۡ مَضَتۡ سُنَّتُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 8

وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُۥ لِلَّهِۚ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 8

وَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَوۡلَىٰكُمۡۚ نِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ. info
التفاسير: