ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمهه‌ى هوساوى - ابوبكر جومى

شماره صفحه:close

external-link copy
26 : 8

وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ أَنتُمۡ قَلِيلٞ مُّسۡتَضۡعَفُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ تَخَافُونَ أَن يَتَخَطَّفَكُمُ ٱلنَّاسُ فَـَٔاوَىٰكُمۡ وَأَيَّدَكُم بِنَصۡرِهِۦ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 8

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَخُونُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ وَتَخُونُوٓاْ أَمَٰنَٰتِكُمۡ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 8

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurin Sa, akwai ijãra mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 8

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِن تَتَّقُواْ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّكُمۡ فُرۡقَانٗا وَيُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 8

وَإِذۡ يَمۡكُرُ بِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيُثۡبِتُوكَ أَوۡ يَقۡتُلُوكَ أَوۡ يُخۡرِجُوكَۚ وَيَمۡكُرُونَ وَيَمۡكُرُ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ

Kuma a lõkacin da waɗanda* suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci. info

* Ƙuraishãwa suka tãru sunã shãwarar yadda zã su yi da Muhammadu; kõ su ɗaure shi a cikin gida, kõ su kashe shi, kõ su kõre shi. Ra'ayinsu ya tsaya ga su kashe shi da zãɓaɓɓun mutãne daga kõwace ƙabĩla yadda danginsa, Banĩ Hãshim, bã su iya faɗa da dukkan Lãrabãwa, har su kõma ga diyya. A rãnar da suka shirya kashe shi, Allah Ya umurce shi da hijira zuwa Madĩna. A lõkacin da ya fita daga gidansa ya iske su tsaitsaye, sunã barci, ya zuba turɓãya a kunnuwansu, sa'annan ya shige suka tafi tãre da Abũbakar, suka sauka a cikin kõgon dũtsen Thaur. Bãyan kwãnaki uku, suka fita zuwa Madina.

التفاسير:

external-link copy
31 : 8

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا قَالُواْ قَدۡ سَمِعۡنَا لَوۡ نَشَآءُ لَقُلۡنَا مِثۡلَ هَٰذَآ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko." info
التفاسير:

external-link copy
32 : 8

وَإِذۡ قَالُواْ ٱللَّهُمَّ إِن كَانَ هَٰذَا هُوَ ٱلۡحَقَّ مِنۡ عِندِكَ فَأَمۡطِرۡ عَلَيۡنَا حِجَارَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ أَوِ ٱئۡتِنَا بِعَذَابٍ أَلِيمٖ

A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi." info
التفاسير:

external-link copy
33 : 8

وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمۡ وَأَنتَ فِيهِمۡۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ مُعَذِّبَهُمۡ وَهُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ

Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu,* kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri. info

* Rãyuwar Annabi a cikin mutãne aminci ne daga azãba, haka kuma yin istigfãri aminci ne. Wanda ke son wadãta da aminci daga Allah, sai ya lazimci istigfãri da bin sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

التفاسير: