* Anã amfãni da dabbar hadaya wajen hawa sabõda larũra da shan nõno har a kai ga wurin sõke ta. Anã sõke hadaya a cikin hurumin Makka.
* Waɗannan sũ ne siffõfin mãsu ƙasƙantar da kai watau mãsu tawãli'u. Zukãtansa na firgita idan an ambaci Allah, su ga kamar sunã ganin sa, a gaba gare su, sabõda haka sai su ji sauƙin haƙuri ga ɗaukar masifa, kuma su tsayar da salla da sauran ibãdõdi na jiki kuma su bãyar da zakka da sauran ibãdõdin dũkiya.
* Wannan yanã nũna yadda ake sũkar rãƙuma sunã tsaye a kan ƙafãfu uku a ɗaure guda bãyan an lanƙwasa guiwarta an ɗaure sama. Anã ambatar sũnan Allah kuma a yi kabbara a lõkacin sũkar a masõkar zũciyarta. Anã sukar shãnu kuma anã yankansu. Anã yankan tumãki da awaki kawai. Anã yanka sauran dabbõbi da tsuntsaye kawai.
* Allah Yã yi alkawarin kãre wanda yake aiki da taƙawa dõminsa. Yanã tunkuɗe masa maƙiyansa, Ya yi masa faɗa.