ترجمهٔ معانی قرآن کریم - ترجمهه‌ى هوساوى - ابوبكر جومى

Alhajj

external-link copy
1 : 22

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيمٞ

Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar* ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma. info

* Addĩni tsantsa shĩ ne ke sanya ƙafa ta tsaya da kyau. Idan an cũɗanya addĩni da wasu abũbuwa na bidi'a kõ al'ãdu, to, ƙafa bã ta iya tsayi balle ma a lõkacin girgizar ƙasã ta tsayin Sa'a.

التفاسير:

external-link copy
2 : 22

يَوۡمَ تَرَوۡنَهَا تَذۡهَلُ كُلُّ مُرۡضِعَةٍ عَمَّآ أَرۡضَعَتۡ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمۡلٍ حَمۡلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَٰرَىٰ وَلَٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٞ

A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 22

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيۡطَٰنٖ مَّرِيدٖ

Akwai daga mutãne* wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai. info

* An raba mutãne a game da addĩni kashi huɗu, sa'annan ya fãra da kashi na farko mafi yawa daga cikin sauran kasũsuwan, watau kashin wãwãye mãsu biyar Shaiɗan ga al'ãdu da son zũciyõyi su bar hukunce-hakuncen Allah.

التفاسير:

external-link copy
4 : 22

كُتِبَ عَلَيۡهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهۡدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 22

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ

Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa. info
التفاسير: