Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy

Al'dour

external-link copy
1 : 52

وَٱلطُّورِ

Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã). info
التفاسير:

external-link copy
2 : 52

وَكِتَٰبٖ مَّسۡطُورٖ

Da wani littãfi rubũtacce. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 52

فِي رَقّٖ مَّنشُورٖ

A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 52

وَٱلۡبَيۡتِ ٱلۡمَعۡمُورِ

Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda). info
التفاسير:

external-link copy
5 : 52

وَٱلسَّقۡفِ ٱلۡمَرۡفُوعِ

Da rufin nan da aka ɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 52

وَٱلۡبَحۡرِ ٱلۡمَسۡجُورِ

Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa). info
التفاسير:

external-link copy
7 : 52

إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٞ

Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 52

مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٖ

Bã ta da mai tunkuɗẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 52

يَوۡمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوۡرٗا

Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 52

وَتَسِيرُ ٱلۡجِبَالُ سَيۡرٗا

Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 52

فَوَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 52

ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي خَوۡضٖ يَلۡعَبُونَ

Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 52

يَوۡمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا

Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 52

هَٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." info
التفاسير: