Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy

Al'ahkab

external-link copy
1 : 46

حمٓ

Ḥ. M̃. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 46

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 46

مَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَمَّآ أُنذِرُواْ مُعۡرِضُونَ

Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi). info
التفاسير:

external-link copy
4 : 46

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya." info
التفاسير:

external-link copy
5 : 46

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu? info
التفاسير: