* Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kuma bai fita ba daga tsãrin cewa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura.
* Talakãwa mutãne ne mãsu rauni a cikin hannuwan shugabanninsu. Su da dukiyarsu amãnõni ne na Allah a cikin hannuwan shugabanni, saboda haka tsaronsu da dukiyarsu, gwargwadon shari'a, da yin hukunci a tsakaninsu da ãdalci, bãyar da amãna ne ga mãsu ita.Wanda ya bi son zuciyarsa duka ga ɗayan waɗannan abũbuwa, to, yã yi yaudara ga Allah ke nan. Allah kuma zai kama shi da hukuncin mayaudari.
* Haka su kuma mutãne talakãwa, amãna ce a kansu su yarda da hukuncin Allah da Manzonsa, a kome na al'amurransu da mu'ãmalõlinsu. Kuma wãjibi ne a kansu su yarda da abin da aka hukunta a kansu daidai da sharĩ'ar Allah. Su kuma idan sun sãɓa, to, sun yaudari amãnar Allah ke nan.