* A lõkacin da aka fãra Yãƙin Uhdu Musulmi suka fãra kõra sunã kisa sunã kãmu. Sai wasu maharba suka ce: "Kada a kãme ganĩma a bar mu," Shugabansu Abdullahi bn Jubair ya ce musu, "Ku tuna da maganar Manzon Allah da ya ce kada mu bar wurinmu sai idan shi ne ya kirãye mu." Sai suka ƙi saurãran maganarsa suka tafi kãmun ganima. Sai Allah Ya biyõ musu da Khãlid bn walĩd ta bãya, ya kashe Abdullahi da sauran waɗanda suka rage. Sa'an nan kuma sai yãƙĩn Musulmi ya karye, suka gudu suka hau dũtse, sai mutum gõma sha ɗaya ko shã biyu kawai aka bari tãre da Annabi, yana kiran su sunã gudu.
* Bãyan da hankalinsu ya kõma gare su sai suka ga sakamakon sãɓãwa umurnin Allah, ya zama karyewar yãƙi da rashin ganĩma.