Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy

Número de página:close

external-link copy
62 : 2

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba*, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba. info

* Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, "Mun kõma garesu" Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musulunci sunã cewa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su.

التفاسير:

external-link copy
63 : 2

وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱذۡكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku. info
التفاسير:

external-link copy
64 : 2

ثُمَّ تَوَلَّيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۖ فَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra." info
التفاسير:

external-link copy
65 : 2

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعۡتَدَوۡاْ مِنكُمۡ فِي ٱلسَّبۡتِ فَقُلۡنَا لَهُمۡ كُونُواْ قِرَدَةً خَٰسِـِٔينَ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu." info
التفاسير:

external-link copy
66 : 2

فَجَعَلۡنَٰهَا نَكَٰلٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهَا وَمَا خَلۡفَهَا وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
67 : 2

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تَذۡبَحُواْ بَقَرَةٗۖ قَالُوٓاْ أَتَتَّخِذُنَا هُزُوٗاۖ قَالَ أَعُوذُ بِٱللَّهِ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai." info
التفاسير:

external-link copy
68 : 2

قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِيَۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ لَّا فَارِضٞ وَلَا بِكۡرٌ عَوَانُۢ بَيۡنَ ذَٰلِكَۖ فَٱفۡعَلُواْ مَا تُؤۡمَرُونَ

Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku." info
التفاسير:

external-link copy
69 : 2

قَالُواْ ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوۡنُهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٞ صَفۡرَآءُ فَاقِعٞ لَّوۡنُهَا تَسُرُّ ٱلنَّٰظِرِينَ

Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta." info
التفاسير: