Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

Al'muzammil

external-link copy
1 : 73

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُزَّمِّلُ

Yã wanda ya lulluɓe! info
التفاسير:

external-link copy
2 : 73

قُمِ ٱلَّيۡلَ إِلَّا قَلِيلٗا

Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 73

نِّصۡفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصۡ مِنۡهُ قَلِيلًا

Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 73

أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا

Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 73

إِنَّا سَنُلۡقِي عَلَيۡكَ قَوۡلٗا ثَقِيلًا

Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 73

إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيۡلِ هِيَ أَشَدُّ وَطۡـٔٗا وَأَقۡوَمُ قِيلًا

Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 73

إِنَّ لَكَ فِي ٱلنَّهَارِ سَبۡحٗا طَوِيلٗا

Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 73

وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلۡ إِلَيۡهِ تَبۡتِيلٗا

Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 73

رَّبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذۡهُ وَكِيلٗا

Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 73

وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهۡجُرۡهُمۡ هَجۡرٗا جَمِيلٗا

Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 73

وَذَرۡنِي وَٱلۡمُكَذِّبِينَ أُوْلِي ٱلنَّعۡمَةِ وَمَهِّلۡهُمۡ قَلِيلًا

Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 73

إِنَّ لَدَيۡنَآ أَنكَالٗا وَجَحِيمٗا

Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 73

وَطَعَامٗا ذَا غُصَّةٖ وَعَذَابًا أَلِيمٗا

Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 73

يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلۡجِبَالُ كَثِيبٗا مَّهِيلًا

Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 73

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ رَسُولٗا شَٰهِدًا عَلَيۡكُمۡ كَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ رَسُولٗا

Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo* mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo** zuwaga Fir'auna, info

* Wato Annabi Muhammad, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.** Wato Annabi Mũsã, aminci ya tabbata a gare shi.

التفاسير:

external-link copy
16 : 73

فَعَصَىٰ فِرۡعَوۡنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذۡنَٰهُ أَخۡذٗا وَبِيلٗا

Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 73

فَكَيۡفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرۡتُمۡ يَوۡمٗا يَجۡعَلُ ٱلۡوِلۡدَٰنَ شِيبًا

To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 73

ٱلسَّمَآءُ مُنفَطِرُۢ بِهِۦۚ كَانَ وَعۡدُهُۥ مَفۡعُولًا

Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 73

إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا

Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa. info
التفاسير: