Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

Al'haqah

external-link copy
1 : 69

ٱلۡحَآقَّةُ

Kiran gaskiya! info
التفاسير:

external-link copy
2 : 69

مَا ٱلۡحَآقَّةُ

Mẽne ne kiran gaskiya? info
التفاسير:

external-link copy
3 : 69

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَآقَّةُ

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? info
التفاسير:

external-link copy
4 : 69

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ

Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! info
التفاسير:

external-link copy
5 : 69

فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِيَةِ

To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 69

وَأَمَّا عَادٞ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٖ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٖ

Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 69

سَخَّرَهَا عَلَيۡهِمۡ سَبۡعَ لَيَالٖ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومٗاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِيهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِيَةٖ

(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 69

فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٖ

To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? info
التفاسير: