Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

external-link copy
90 : 5

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a*, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara. info

* Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i (ƙarya), da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan.

التفاسير: