Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

Page Number:close

external-link copy
109 : 3

وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra. info
التفاسير:

external-link copy
110 : 3

كُنتُمۡ خَيۡرَ أُمَّةٍ أُخۡرِجَتۡ لِلنَّاسِ تَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَتَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَتُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِۗ وَلَوۡ ءَامَنَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۚ مِّنۡهُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawan su fãsiƙai ne. info
التفاسير:

external-link copy
111 : 3

لَن يَضُرُّوكُمۡ إِلَّآ أَذٗىۖ وَإِن يُقَٰتِلُوكُمۡ يُوَلُّوكُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãƙe ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba. info
التفاسير:

external-link copy
112 : 3

ضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ أَيۡنَ مَا ثُقِفُوٓاْ إِلَّا بِحَبۡلٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَحَبۡلٖ مِّنَ ٱلنَّاسِ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَسۡكَنَةُۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi. info
التفاسير:

external-link copy
113 : 3

۞ لَيۡسُواْ سَوَآءٗۗ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ أُمَّةٞ قَآئِمَةٞ يَتۡلُونَ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ وَهُمۡ يَسۡجُدُونَ

Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada. info
التفاسير:

external-link copy
114 : 3

يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai. info
التفاسير:

external-link copy
115 : 3

وَمَا يَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلَن يُكۡفَرُوهُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu taƙawa. info
التفاسير: