Translation of the Meanings of the Noble Qur'an - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

Page Number:close

external-link copy
137 : 26

إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ

"Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko." info

* Wãtau lãbarun mutãne waɗanda ba su ci gaba ba bã su son a yi rawa da nishãɗi. Anã karantawar ma'anar ƙaryar ta farko, watau wai tãtsũniya ce: a ce wai a hana ãyã akan tsaunuka dõmin wasanni. Suna nufi da ãya ko alãma gidãjen rawa da na nashãdi watau stadiyam da kasĩno.

التفاسير:

external-link copy
138 : 26

وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ

"Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." info
التفاسير:

external-link copy
139 : 26

فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
140 : 26

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
141 : 26

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
142 : 26

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?" info
التفاسير:

external-link copy
143 : 26

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

"Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce." info
التفاسير:

external-link copy
144 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. info
التفاسير:

external-link copy
145 : 26

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
146 : 26

أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ

"Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?" info

* Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi.

التفاسير:

external-link copy
147 : 26

فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ

"A cikin gõnaki da marẽmari." info
التفاسير:

external-link copy
148 : 26

وَزُرُوعٖ وَنَخۡلٖ طَلۡعُهَا هَضِيمٞ

"Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki?" info

* Hirtsi shi ne 'ya'yan itãce sãbabbi tun ba su nuna ba. Wãtau hirtsin gonakinsu idan an ci shi narkewã ya ke yi a cikin ciki, balle kuma 'ya'yan itãce nunannu.

التفاسير:

external-link copy
149 : 26

وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا فَٰرِهِينَ

"Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?" info
التفاسير:

external-link copy
150 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
151 : 26

وَلَا تُطِيعُوٓاْ أَمۡرَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

"Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata." info
التفاسير:

external-link copy
152 : 26

ٱلَّذِينَ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ

"Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
153 : 26

قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ

Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake." info
التفاسير:

external-link copy
154 : 26

مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

"Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya." info
التفاسير:

external-link copy
155 : 26

قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٞ لَّهَا شِرۡبٞ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ

Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne." info

* Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi.

التفاسير:

external-link copy
156 : 26

وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

"Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku." info
التفاسير:

external-link copy
157 : 26

فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ

Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma. info
التفاسير:

external-link copy
158 : 26

فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
159 : 26

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. info
التفاسير: