Übersetzung der Bedeutungen von dem heiligen Quran - Die Übersetzung in Hausa - Abu Bakr Jomy.

Nummer der Seite:close

external-link copy
249 : 2

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّٰبِرِينَ

A lõkacin da ¦ãlũta ya fita* da rundunõnin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (¦ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa."Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri." info

* Sõja na bukãtar tarbiya, su sãbã da wahala da ƙishirwa da magana mai shiryarwa. Kõgin kuwa shĩ ne kõgin Urdun tsakãnin Urdun da Falastĩn.

التفاسير:

external-link copy
250 : 2

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma a lõkacin da suka* bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." info

* Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnen Badar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.

التفاسير:

external-link copy
251 : 2

فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai. info
التفاسير:

external-link copy
252 : 2

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni. info
التفاسير: