Prijevod značenja časnog Kur'ana - Prijevod na Hausa jezik - Ebu Bekr Džumbi

Al'balad

external-link copy
1 : 90

لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba. info

* Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu.

التفاسير:

external-link copy
2 : 90

وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 90

وَوَالِدٖ وَمَا وَلَدَ

Da mahaifi da abin da ya haifa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 90

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ

Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 90

أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٞ

Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? info
التفاسير:

external-link copy
6 : 90

يَقُولُ أَهۡلَكۡتُ مَالٗا لُّبَدًا

Yana cẽwa "Na* halakarda dũkiya mai yawa," info

* Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni.

التفاسير:

external-link copy
7 : 90

أَيَحۡسَبُ أَن لَّمۡ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ

Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? info
التفاسير:

external-link copy
8 : 90

أَلَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ عَيۡنَيۡنِ

Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? info
التفاسير:

external-link copy
9 : 90

وَلِسَانٗا وَشَفَتَيۡنِ

Da harshe, da leɓɓa biyu. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 90

وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ

Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba? info

* Hanyar alheri da ta sharri.

التفاسير:

external-link copy
11 : 90

فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ

To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? info
التفاسير:

external-link copy
12 : 90

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ

Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? info
التفاسير:

external-link copy
13 : 90

فَكُّ رَقَبَةٍ

Ita ce fansar wuyan bãwa. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 90

أَوۡ إِطۡعَٰمٞ فِي يَوۡمٖ ذِي مَسۡغَبَةٖ

Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 90

يَتِيمٗا ذَا مَقۡرَبَةٍ

Ga marãya ma'abũcin zumunta. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 90

أَوۡ مِسۡكِينٗا ذَا مَتۡرَبَةٖ

Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 90

ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡمَرۡحَمَةِ

Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 90

أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ

Waɗannan ne ma'abũta albarka* info

* Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira.

التفاسير:

external-link copy
19 : 90

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ

Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci* info

* Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira.

التفاسير:

external-link copy
20 : 90

عَلَيۡهِمۡ نَارٞ مُّؤۡصَدَةُۢ

A kansu akwai wata wuta abar kullewa. info
التفاسير: