* Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa.
* A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen Manzon Sa.
* Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su.
* Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka.
* Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu.
* Waɗanda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amuransu da kyau, kuma zai wadãta su a dũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya.