Prijevod značenja časnog Kur'ana - Prijevod na Hausa jezik - Ebu Bekr Džumbi

Broj stranice: 536:534 close

external-link copy
77 : 56

إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ

Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. info
التفاسير:

external-link copy
78 : 56

فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ

A cikin wani littafi tsararre. info
التفاسير:

external-link copy
79 : 56

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ

Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. info
التفاسير:

external-link copy
80 : 56

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta. info
التفاسير:

external-link copy
81 : 56

أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ

Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa? info
التفاسير:

external-link copy
82 : 56

وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ

Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)? info
التفاسير:

external-link copy
83 : 56

فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ

To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). info
التفاسير:

external-link copy
84 : 56

وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ

Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo. info
التفاسير:

external-link copy
85 : 56

وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ

Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani. info
التفاسير:

external-link copy
86 : 56

فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ

To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba? info
التفاسير:

external-link copy
87 : 56

تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.* info

* Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa.

التفاسير:

external-link copy
88 : 56

فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta, info
التفاسير:

external-link copy
89 : 56

فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ

Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima. info
التفاسير:

external-link copy
90 : 56

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma, info
التفاسير:

external-link copy
91 : 56

فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma. info
التفاسير:

external-link copy
92 : 56

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ

Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun, info
التفاسير:

external-link copy
93 : 56

فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ

Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi. info
التفاسير:

external-link copy
94 : 56

وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ

Da ƙõnuwa da Jahĩm, info
التفاسير:

external-link copy
95 : 56

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ

Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni. info
التفاسير:

external-link copy
96 : 56

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ

Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci. info

* A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cewa: "Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih." Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa.

التفاسير: