* Bayãnin siffõfin mũminai, waɗanda suke tsare su, Yana lãmunce zama haɗe, da gamuwar Musulmi, sũ ne siffõfi shida, nisantar manyan zunubbai da zina, da gãfarta fushi, da tsayar da salla, da shãwara ga al'amuran tsakãninsu, da ciyar da dũkiya da ta wajabci mutum ya ciyar da ita a cikin alheri ga inda Allah Ya ce a ciyar da ita.
* Wajen rãma zãlunci kõ yinsa, mutãne sun kasu kashi huɗu. Mãsu rãmãwa gwargwadon zãlunci, bã su da laifi; da mãsu rãmãwa da abin da ya fi laifin da aka yi musu, to, sunã da laifi kamar mãsu fãra zãlunci, da mãsu gãfartãwa, waɗannan sũ ne Allah ke so.
* Bayãnin mai zãlunci da sakamakonsa a Rãnar Lãhira.