* Yahaya dan zakariyya, shi ne Annabi da aka bai wa hukunci tun yanã yãro. Kuma Shĩ ne mai bãyar da bushãra da Ĩsa, amincin Allah ya tabbata agare su.
* An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne.
* Malã'ikin da ya je ga Maryama a cikin sũrar mutum jibrĩlu ne Yã hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi ciki da Ĩsa.
* Annabi Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya fãra magana ga uwarsa tun a lõkacin da aka haife shi yanã a ƙarƙashin uwarsa. Gudãnar ruwan marmaro a ƙarƙashinta da fitar da 'ya'yan dabĩno dagakututturen dabĩno, alãmu ne mãsu nũna cħwa Allah nã iya halitta jãrĩri bã da uba ba, kuma Yanã tãyar da matattu daga kabarinsu bã da wata wahala ba.