* Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cewa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cewa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Sake al-munkar wãjibi ne a cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtar da hukuncin da ya fi tsanani.
* Watau wani kamfani ne na matalauta, sunã sana'ar ɗaukar kãya a cikin teku, sharika watau kamfani ciniki ya halatta da sharuɗɗansa.
* Wannan ya nũna cewa kirkin uba yanã amfãnin ɗiyansa, haka gari na daraja sabõda sãmun mutãnen kirki a cikinsa, kamar yadda yake ƙasƙanta da ƙasƙancin mazaunansa bisa dalĩlin da farko an kira garin 'alƙarya' sabõda rõwar mazauna, kuma aka kira shi Madĩna sabõda darajar yãran nan biyu da ubansu da taskarsu. Alƙarya ita ce ƙaramin gari watau ƙauye, kuma Madĩna ita ce babban gari.
* Zulƙarnaini an ce sarki ne yanã bin shari'ar lbrãhĩm, ga hannunsa ya musulunta sunansa Askandar. Haliru wazirin sane yanã tafiya a gaban yãƙinsa, kuma ɗan innarsa, watau ɗan khãlarsa ne. Shi ne ya gĩna Askandariyya. Sai dai ga maganar akwai warware jũna. Allah Ya sani. Abin da ke a gabãninmu a nan shĩ ne sanin cħwa Allah Yã bã shi mulki, ya kõ yi shĩ bisa sharĩ'a, ya yi ƙarfi, da ƙarfin Allah.